Kun ga jadawalin zabukan Nigeria kuwa?

Image caption INEC ta ce zaben shugaban kasa za a fara yi

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta fitar da jadawalin zabukan da za a yi a shekarar 2015.

A wata sanarwa da ta fitar, INEC ta ce za a yi zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya ne ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Kazalika, hukumar ta ce za a yi zabukan gwamnoni da 'yan majalisar jihohi ranar 28 ga watan Fabrairu.

Ta kara da cewa za ta fitar da sunayen mutanen da jam'iyyu suka mika mata domin yin takarar shugabancin kasar da na majalisar dokokin tarayya a ranar 13 ga Janairu, sannan ta fitar da sunayen wadanda za su yi takarar gwanoni da 'yan majalisar jihohi ranar 27 ga watan na Janairu, 2015.

Za a je zagaye na biyu ne kwanaki bakwai bayan na farko

INEC ta bayyana cewa ranar 30 ga watan Disamba ce ranar karshe da jam'iyyu za su mika mata sunayen 'yan takarar shugabancin kasar da na 'yan majalisar dokokin tarayyar da suka sauya, yayin da 13 ga watan Janairu za ta kasance ranar karshe da za a sauya sunayen 'yan takar gwamnoni da na majalisun johohi.

Hukumar zaben ta ce za a kammala yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya ne ranar 12 ga watan na Fabrairu, yayin da za a gama kamfe na kujerun gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi ranar 26 ga watan na Fabrairu.

Haka kuma hukumar zaben ta Najeriya ta ce za a yi zabe karo na biyu na kujerar shugaban kasa da kujerun gwamnoni kwanaki bakwai bayan an yi na farko kamar yadda kudin tsarin mulkin kasar ta tanadar.