Matar Marigayi Cif Abiola ta kalubalanci PDP

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Jam'iyyar PDP ta tsaida Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takararta na Shugaban kasa a zaben 2015

A Najeriyar Yayin da wa'adin da hukumnar zaben kasar INEC ta debawa jam'iyun kasar na damar da suke da ita ta sauya 'yan takararsu ke cika ranar talata, rahotanni sun ce jam'iyyu 11 ne su ka tsaida 'yan takarar shugabancin-kasar a zaben na badi.

Sai dai matar da ta nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriyar a karkashin jam'iyyar PDP mai mulki, ta ce har yanzu ba ta cire rai ba, duk kuwa da cikar wannan wa'adi.

Farfesa Akasoba Zainab Duke Abiola dai ta yi zargin cewa jam'iyar PDP ta ki saida mata fom din takarar shugaban kasar, kuma ta ce babu inda aka taba yin haka a duniya.

'Kowa da kowa a Nigeria na da damar ya sayi fom, fom kawai nace su bani su ka ki, mai yasa suke jin tsoro, ni mace ce, ba ni da wani karfi' in ji farfesa Akasoba Zainab Abila

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ne dai zai yi wa jam'iyyar PDP takarar shugabancin kasar a zaben 2015.