AirAsia: Ana ci gaba da gano gawawwaki a teku

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana ci gaba da aikin gano gawawwaki a cikin teku

Kamfanin jiragen sama na AirAsia, ya ce tarkacen da aka gano a cikin tekun na jirgin fasinjarsa ne da ya yi batan dabo a ranar Lahadi.

Jirgin na AirAsia dauke da mutane 162 ya bace ne a kan hanyarsa daga Surabaya na Indonesia zuwa Singapore.

Shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo ya je wurin da jirgin ya yi hadarin inda aka gano gawawwaki da dama.

Mr Widodo ya ce zai aike da karin jiragen ruwan soji wurin, inda igiyar tekun ke kawo cikas wajen ci gaba da laluben.

A na shi bangaren shugaban kamfanin AirAsia Tony Fernandes, ya ce ya kadu ainun da hadarin jirgin kuma ya yi alkawarin taimakawa 'yanuwan wadanda hadarin ya rutsa da su.