AirAsia: An gano gawawwaki 40 a cikin teku

Image caption Iyalan fasinjoji na cikin zullumi

An gano gawawwakin mutane 40 a cikin teku tare da tarkacen jirgin saman AirAsia da ya bace, in ji rundunar ruwan Indonesia.

Masu bincike sun gano gawawwakin da tarkacen jirgin saman suna yawo a saman tekun Java a yankin Borneo na Indonesia.

A ranar Lahadi ne jirgin AirAsia dauke da mutane 162 ya bace a kan hanyarsa daga Surabaya na Indonesia zuwa Singapore.

Masu bincike na kasa da kasa sun shafe kwanaki uku suna kokarin gano inda jirgin saman ya fadi.

Iyalan fasinjojin sun nuna kaduwa bayan da suka ga hotunan gawawwaki sun taso a kan ruwa.