An murkushe yunkurin juyin mulki a Gambia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a shekarar 1994, Mr Jammeh ya ke jan ragamar Gambia

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya ce dakarunsa sun yi nasarar murkushe yunkurin juyin mulki a kasar.

A wata sanarwa, shugaba Jammeh ya ce wani tsohon kwamandan dakarun kasar Lamin Sanne ne ya kutsa cikin kasar tare da wasu 'yan bindiga, suka kuma kai hari kan fadar shugaban kasar da ke birnin Banjul.

Rahotani dai an cewa an kwashe tsawon dare ana jin amon munanan barin wuta kusa da fadar shugaban kasar.

Lamarin ya faru ne yayinda shugaban kasar Yahya Jammeh ke wata ziyarar aiki a Faransa.

Shugaban ya ce an hallaka hudu daga cikin 'yan bindigar.

Shugaba Jammeh ya kara da cewa zai dawo daga ziyara aikin da ya kai kasar Faransa, don duba yadda za a gudanar da bincike game da yunkurin juyin mulkin.