Ba a biya ma'aikata 70,000 albashinsu ba

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Nigeria na fuskantar zabe a shekara ta 2015

Kimanin ma'aikata dubu 70 ne a Nigeria su ka yi bukukuwan kirsimeti a cikin halin rashi sakamakon rashin biyan su albashi da gwamnatin tarayya ta yi har na tsawon watanni uku.

Tuni dai kungiyar manyan ma'aikatan kasar ta ce za ta dauki mataki idan al'amarin ya wuce gona da iri.

Ma'aikatan su kimanin dubu 70 sun fito ne daga ma'aikatu 30 ciki hada da ma'aikatar ayyuka da ta kwadago da ta ilimi da kuma ma'aikatun wutar lantarki da ta ma'adanai da karafa.

Babban sakataren kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati na kasa, Mista Alade Lawal ya ce "Ma'aikata da dama ba su samu albashi ba tun watan Oktoba kuma sun dade su na yin alkawari cewa za su biya kafin bikin kirsimeti amma har yanzu ko taro ba su gani ba."

Kawo yanzu gwamnatin kasar ba ta ce komai ba game da lamarin.