An gano jirgin da aka sace a Najeriya

Image caption An sace jirgin ruwan yakin ne a Bayelsa

A Najeriya, jami'an tsaron kasar sun ce sun gano jirgin ruwan yakin nan da ake zargin 'yan fashin teku sun sace a kwanakin baya a jihar Bayelsa.

Rundunar sintiri ta hadin gwiwa ta shaidawa BBC cewa ta gano wurin da aka yi watandar jirgin, da kuma wasu daga cikin makaman da ke cikinsa.

Kakakin rundunar, Kanar Mustapha Abubakar Anka, ya ce "an gano inda suka fatattaka shi, suka cire bindiga da inji da baturan da ke jikinsa. Bindigarsa kuma da aka sace, sun binne ta a harabar wata coci. A wasu wuraren kuma, an gano manya manyan bindigogi guda uku da AK 47 guda daya..."

A cewarsa, an kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu a sace jirgin, amma ba a gano sojoji ukun da suka bata ba.