An kwantar da Sarkin Saudiyya a asibiti

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarki Abdullah, mai shekaru 90 a duniya, ya hau sarautar kasar ne a shekarar 2005.

An kwantar da Sarki Abdullah na Saudi Arabia a wani asibiti domin yi masa gwaje-gwaje.

Sanarwa da gidan sarautar kasar ya fitar dai ba ta yi cikakken bayani kan halin da yake ciki ba.

Hannayen jari a kasuwar shunku ta kasar sun fadi jim kadan da jin wannan labari, wanda kafar watsa labaran gwamnatin kasar ta bayar.

Sarki Abdullah, mai shekaru 90 a duniya, ya hau sarautar kasar ne a shekarar 2005.