Juyin mulki: Yahya Jammeh ya koma Gambia

Hakkin mallakar hoto online
Image caption Jammeh ya hau mulki ne a 1994 bayan ya yi juyin mulki

Rahotanni daga Gambia na cewa shugaba Yahya Jammeh ya koma kasar, kwana guda bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi.

A ranar Laraba, shugaban ya ce wani tsohon dakarun tsaron kasar, Lamin Sanneh ya jagoranci yunkurin yin juyin mulki, inda ya kaddamar da hari kan fadar shugaban kasa da ke birnin Banjul.

Babu dai cikakken bayani kan kasar da Mr Jammeh ya tafi -- wasu na cewa ya je Faransa, yayin da wasu ke cewa Dubai ya je.

Mr Jammeh ya dare kan karagar mulkin kasar ce bayan wani juyin mulki da ya jagoranta shekarar 1994.