Za a sake shari'ar 'yan Al-Jazeera a Masar

Zanga zangar neman sakin yan aljazeera da aka daure a Masar
Image caption Zanga zangar neman sakin yan aljazeera da aka daure a Masar

Kotun Kolin Masar ta ce a sake gudanar da shara'ar da ta kai ga daure wasu 'yan jaridar gidan talabijin na Al-jazeera saboda taimakawa kungiyar 'yan uwa Musulmi da aka haramta a kasar.

Mutanen --da suka hada tsohon ma'aikacin BBC Peter Greste--an daure su ne daga shekaru bakwai zuwa goma.

Chris Flynn lauyan da ke kare Mr Greste yace, duka dai za a iya cewa abun zai yiwa Peter Greste dadi.

Ya ce, ba dai an wanke shi ne kamar yadda muka yi tsammani ba, amma kuma hakan na nuna cewa shara'ar farkon cike take da kura-kurai.

Mr Flynn ya ce muna sa ran hakan zai baiwa shugaban Masar damar bada umarnin fitar da shi daga kasar.

Za su ci gaba da zama a kurkuku har sai an fara sabuwar shara'ar.

Wakilin BBC a Birnin Al-kahira ya ce shara'ar na yin babbar illa ga mutuncin kasar , kuma akwai alamun cewa hukumomin kasar na son su kawo karshen matsalar cikin gaggawa.