An karrama Baylis da lambar yabo

Ayyukan masu kirkire-kirkire Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ayyukan masu kirkire-kirkire

Travor Baylis wanda ya kirkiro wani radiyo da ake yi ma wani ya samu lambar yabo ta CBE a jerin mutanen da aka karrama da lambar yabo ta sabuwar shekara.

Sunan da ya yi saboda kirkirar radiyon Baygen da ake yi ma wani ta sanya Mr Baylis ya samu lambar yabo saboda ayyukansa na daukaka ilimi.

A tsawon rayuwarsa wadda ke cike da kirkirar ayyuka na kawa na hannu, Mr Baylis ya mayar da hankalinsa ga kirkire-kirkire da ayyuka na injiniya.

A baya-baya nan ya yi fafutukar mayar da Ingila ta zamo kyakkyawan wurin zama na mutane masu kirkire-kirkire, yana kuma taimakonsu wajen kare abubuwan da suke kirkira.

"wani babban abin mamaki ne, kamar yadda Mr Baylis wanda ya fito daga yankin Twickenham ya fada, samun labarin da na yi na wannan kyauta. "na samu OBE a shekarar 1997, wannan kuma ya zamo wani lokaci da na ji matukar dadi a rayuwa ta."

Ina ta kokarin matsawa wajen taimakon sauran masu kirkire-kirkire saboda da yawa daga cikinsu a kan kwace fasaharsu kamar a Turkiyya, ko kuma su ga cewar ba su da kudin da za su biya lauyoyi da za su kare su.

A halin da ake ciki, Mr Baylis yana jan ragamar wani kamfani ne da ake kira Baylis Brands - wanda ke bayar da shawara ga masu kirkire-kirkire kyakkyawar hanyar da za su yi tunanin wasu hanyoyi na yin wasu abubuwa da kuma tura su ga kwararru wadanda za su taimaka musu wajen kyautata abinda suka kirkira, a kuma tura shi kasuwanni.

Radiyon da ya kirkira Baygen Radio tana amfani da na'ura ne wadda ake wanawa a maimakon sanya ma ta battir ko kuma a hada ta da wuta.

Yana kuma kokarin ganin an canza dokoki ta yadda za su taimaka wajen kare masu kirkire-kirkire da injiniyoyi, idan suka ci karo da wani wanda ke ci da guminsu.

Babban abinda ya fito da sunan Mr Baylis shine radiyon da ya kirkiro Baygen Wind-up Radio, wanda ya kirkira a shekarar 1991 a yayinda yake kallon wani shiri game da ciwon Kanjamau a Afrika wanda ya ba da shawarar amfani da shire-shiren radiyo don rage yaduwar sa.

Bullar da radiyon na sa ya yi a wani shirin BBC na Tomorrow's World a shekarar 1994 ya taimaka wajen sanya abinda ya kirkiro zama kayan da suka shiga kasuwannin kasashen duniya.

Karin bayani