Chibok: Iyaye sun ce "bamu manta ba"

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kungiyar Bring Back Our Girls dake fafutukar ganin hukumomi sun ceto 'yan matan Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram ta sace sun gudanar da wani taro a Abuja domin matsawa gwamnatin kasar lamba akan ta yunkura don kubutar da 'yan matan.

Taron ya kuma samu halartar wasu daga cikin iyayen 'yan matan da aka sace da wasu 'yan Chibok din mazauna Abuja.

Sun gudanar da taron ne a dandalin Unity Fountain a Abuja, wanda shine asalin matattarar su.

Wani daga cikin iyayan ya shaidawa Sashen Hausa na BBC cewa: "Har yanzu fa bamu manta ba, muna nan akan bakan mu, sai an kawo mana 'ya-'yan mu. Gwamnati ta yi shiru, tunda muka bar gaban shugaban kasa, ranar 22 ga watan Yuli, an barmu kamar mu ba 'yan kasa ba."

A watan Afrilun bara ne Boko Haram ta sace 'yan mata sama da 200 a makarantar sakandiren Chibok dake jihar Borno a arewacin Najeria.

Har yanzu dai gwamnati kasar ta kasa kubutar da su daga hannun 'yan Boko Haram din da ta ce zata saida su a kasuwar bayi.

Lamarin dai ya janyo wa Najeriyar bakin jini a ciki da wajen kasar.