Chibok: 'Iyaye na tunanin zuwa kotu'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu ba bu labarin 'yan matan Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram su ka sace a Nigeria

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan sakandaren Chibok da har yanzu ke hannun 'yan kungiyar Boko Haram na duba yiwuwar kai gwamnatin Nigeria kara kotu saboda zargin cewa ta gaza.

Daya daga cikin iyayen 'yan matan Chibok ya fadawa BBC cewa idan ya samu hadin kai da taimakon lauyoyin da za su kare shi , zai shigar da karar gwamnatin Najeriya a kotu, game da abun da ya kira gazawarta wajen ceto 'ya 'yansu.

Irin wadannan iyaye sun yi zargin cewa gwamnatin Nigeriar ba da gaske take ba wajen ceto 'ya'yannasu

A baya dai wasu iyayen 'yan matan sun taba yin barazanar shiga dajin Sambisa da kansu inda suke zargin nan ne inda 'yan matan suke.

Gwamnatin Nigeria dai na cewa ta na iyakacin kokarinta wajen ganin an ceto 'yan matan da ransu.