China ta kori wani babban jami'in diflomaciyarta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekaru biyu da suka gabata gwamnatin China ta kaddamar da yaki a kan masu sace kudaden gwamnati

China ta ce ta kori wani babban jami'in diplomaciyarta, kuma zata gudanar da bincike akansa.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce ana zargin Zhang Kunsheng da saba dokar da'ar aiki.

Mr Zhang wanda mataimaki ne ga ministan harkokin wajen Chinan, shi ne babban jam'in diplomaciyar kasar mafi girman mukami da ya shiga hannu, a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa a kasar, wanda Shugaba Xi Jinping ya kaddamar shekaru biyu da suka gabata.

An dai kama 'yan siyasa da manyan mutane da dama bayan kaddamar da wannan yaki