Gambia: Shugaba Jammeh ya soma cafke 'yan adawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi harbe harbe a babban birnin kasar a lokacin da Shugaba Jammeh yake kasar Faransa

Rahotanni daga Gambia na cewa an kama mutane da dama bayan zargin da ake na cewa an yi yunkurin yiwa shugaban kasar Yahya Jammeh juyin mulki

An ruwaito cewa dakarun dake biyayya ga Shugaba Jameh sun yi ta bi gida gida suna lalubo 'yan adawa.

Tun da farko, Shugaba Jammeh ya yi zargin cewa wasu 'yan tawaye ne dake samun goyan bayan wasu kungiyoyin kasashen ketare ne ke da alhakin harin na ranar Talata a babban birnin kasar na Banjul.