"Dan-kunar-bakin-wake" ya mutu a Gombe

Harin Bama-bamai a Gombe Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Harin da aka kai kwanan baya a tashar mota a birnin Gomben ya kashe mutane akalla 20

'Yan sanda a Jihar Gombe ta arewa maso gabashin Najeriya sun ce bam din da ya tashi da safiyar yau Alhamis mai yiwuwa wani dan kunar bakin wake ne ke dauke da shi.

Kakakin 'yan sandan Jihar, DSP Fwaje Atajiri, ya shaida wa BBC cewa mutumin, wanda ake kyautata zaton dan kunar bakin wake ne, yana cikin tafiya a kan babur a unguwar Arawa bam din ya tashi da shi.

Tashin bom din na safiyar Alhamis din dai ya biyo bayan fashewar wadansu abubuwa ne da aka zaton bama-bamai a daren jiya a wani barikin soja da ke babban birnin Jihar, wato Gombe.

Har yanzu dai hukumomi ba su yi karin bayani ba a kan tashe-tashen bama-baman na daren ranar Laraba, amma bayanai na cewa rukuni na farko na bama-baman masu karfin gaske, sun tashi ne mintuna kadan a tsakaninsu.

A cewar mazauna birnin na Gombe, daya ya fashe ne kusan karfe takwas na dare, sai kuma aka ji rugugin bam na biyu da karfe takwas da 'yan mintuna.

Su kuwa bama-bamai na rukuni na biyu, an ji karar fashewarsu ne da misalin karfe goma da rabi na dare.

Karin bayani