'PDP na fuskantar rikici a Borno'

Image caption Jam'iyyar PDP na fama da rikici a jihohi da dama

Wata kungiyar al'ummar Borno da ake kira Yerwa - mazauna kudu maso yammacin Najeriya ta gudanar da taro akan matsalolin siyasar PDP a jihar Borno

Kungiyar ta ce ta hango wannan rikici ne da ke tunkarar siyasar jihar bayan na Boko Haram

Hakan dai na zuwa bayan sauya Gambo Lawan dan takarar fidda gwani na jam'iyyar PDP da ya sa mu nasara a zaben, da Mohammed Imam, wani da ake cewa na da goyon bayan tsohon gwamnan jihar , Senato Ali Modu Shariff.

Jihar Borno dai na fama da rikicin Boko Haram.