An gano manyan tarkacen jirgin AirAsia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana ganin gano tarkacen zai ba da kwarin guiwa ga aikin da ake yi na sanin dalilin faduwar jirgin

Jami'an kasar Indonesia sun ce masu aikin ceto sun gano wasu manyan tarkacen jirgin AirAsia, wanda ya tarwatse cikin tekun Java a ranar Lahadi, guda biyu.

Babban jam'in aikin ceton ya ce an gano manyan abubuwan guda biyu ne a karkashin tekun.

Wakilin BBC ya kara da cewa babban jami'in yana kuma da kwarin gwiwar cewa abubuwan da aka gano wani bangare ne na jirgin, kuma idan har hakan ta tabbata, to kuwa an sami gagarumin cigaba a wannan aiki.

An dai tsamo akalla gawawwakin mutane talatin daga cikin mutane 162 da ke cikin jirgin a lokacin da ya yi hadarin.