Faransa za ta saya wa Nijar jirage marasa matuka

Hakkin mallakar hoto
Image caption Nijar na fuskantar kalubalen tsaro saboda makwabtakarta da Nigeria da kuma Libya

A Jamhuriyar Nijar Ministan tsaron kasar Faransa Jean Yves leDrian ya ce gwamnatin kasar Fransa za ta sayawa sojojin Nijar wasu karin jirage marasa matuka guda 3 a kokarin da Faransan ta ke yi na yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Ministan Faransan ya bayyana haka ne jiya a lokacin da ya ziyarci sansanin sojojin Faransan da ke Yamai a wata ziyarar aiki da ta kai shi a kasar.

Nijar na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar kalubalen tsaro saboda rikicin Boko Haram a makwabciyarta Nigeria.

Dubun dubatar 'yan gudun hijira daga Nigeria na rayuwa yanzu haka a wasu sansanoni a Nijar din.