'Ana yi wa matasa dauki dai-dai a Mubi'

Mubi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Mubi na daya daga cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suka kama

A Najeriya, a yayin da al'ummar garin Mubi wanda 'yan Boko Haram suka kwace a kwanakin baya ke ci gaba da komawa garin bayan kwato shi, wasu mazauna garin na zargin jami'an tsaro da kama matasa bisa zargin 'yan Boko Haram ne.

Hakan dai, a cewar mazauna garin, na sa mutane suna kin komawa domin ka da a kama su.

Alhaji Abdurrahman Kwaccam wanda daya ne daga cikin mazauna garin, ya shaida wa BBC cewa sun umarci lauyoyinsu su dauki mataki, a kan lamarin.