Ebola: 'yar Birtaniya na mawuyacin hali

Wata Maka'aikaciyar Jinyar Birtaniya da ta kamu da Ebola a kasar Saliyo na cikin wani mawuyacin hali a cewar jami'an asibitin da aka kwantar da ita.

Wata sanawar daga Royal Free Hospital tace lafiyar Pauline Cafferkey na cigaba da tabarbarewa sannu a hankali a 'yan kwankin nan.

An baiwa Misis Cafferkey wasu magungunan gwaji biyu-- daya na zaburadda da garkuwar jiki, daya kuma ruwan jinin wadanda suka warke daga cutar.

A watan jiya ne dai ta kamu da cutar lokaicinda take aiki da kungiyar agaji ta Save The children

A wani sako da ya aike mata ta twitter, Fry minista David Cameroun ya ce yana taya Pauline Cafferkey da addu'a sakamakon mayuwaycin halin da ta shiga saboda cutar Ebola.

Sakataren kiwon lafiyar Birtaniya ma ya nuna damuwa akan halinda matar ta shiya, inda yace ya tabbata jami'an asibitin na iya kokarin su wajen kulawa da matar

Jirgin da matar ta hau daga Salio, ya bi ta Morocco kafun ya isa London.

Kuma ta fada wa ma'aikatan filin jirgin saman Heathrow cewa kamar tana fama da zazzabi.

Sun gwada zafin jikinta har so bawai a cikin sa'o'i 8 sai suka barta ta wuce Scotland bayan sun ga kamar babu wata matsala

Yanzu jami'an kiwon lafiya na sa alamar tambaya akan ingancin tsarin tantance mutane a filin jirgin saman bayan lamarin.

Da matar ta isa Scotland sai aka ga lafiyar ta ta tabarbare.

Daga nan ne sai aka maida ita London

Jami'ain kiwon lafiya a Scotland din sun ce sun yi magana da duk fasinjoji 71 da suka hau jirgi da matar daga London zuwa Glasgow

Haka nan kuma an tuntubi duk mutane dari-da-daya da suka yi tafiya da ita daga Cassablanca zuwa London.

Matar ita ce ta biyu da aka taba samu da Ebola a Birtaniya.

Mutum na farko shima wani mai aikin agaji ne - William Pooley - amma shi ya samu sauki kuma har an sallame shi a watan Satunban bara.