Na'urori zasu rika kashe kansu a Turai

Image caption Amfani da na'urori masu kashe kansu wani bangare ne na rage dumamar yanayi

Tarayyar Turai ta dauki wasu matakai da zasu sa na'urorin talabijin masu amfani da intanet su rika kashe kansu a lokutan da ba a amfani da su.

Akwai na'urorin talabijin da yawa da ake barin su a kunne a kowanne lokaci, abinda ya sa suke amfani da wutar lantarki daga watt 25 zuwa 100, lokacin da masu su suke barci.

Sabbin na'urorin da za a fara sayar wa daga ranar Alhamis zasu rika kashe kansu idan ba a amfani da su.

Hukumar tarayyar Turai ta ce wadannan matakai zasu rage wa mutane yawan kudaden wuta da suke kashe wa da kimanin Fam 32 a shekara.

Wannan mataki wani bangare ne na kokarin da tarayyar turan ke yi na inganta muhalli, da rage yawan kudaden da ake kashewa da kuma rage yawan hayakin da ake fitarwa mai dumama yanayi.

Matakan sun shafi na'urorin tafasa shayi da sauransu.

Masu kamfanonin kera kayayyaki da suka ki yin aiki da sabbin ka'idojin zasu fuskanci tuhuma daga kasashen tarayyar.