Mutane sun fusata ga toshe Shafin "Jihadi" a India

Internet a India
Image caption Internet a India

Matakin da gwamnati ta dauka na toshe wasu shafukka masu tasiri sama da 30 ya tsokano fushin jama'a a sassa dabam-dabam na kasar India.

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta India ce ta bayar da umurnin a toshe shafukkan don kare buga harkokin 'yan jihadi.

Bayan matsin lamba, an janye toshewar da aka yi ma wasu shafukkan hudu da suka hada Weebly da Vimeo da Daily Motion da Github.

Jami'ai sun ce za a janye toshewar da aka yi ma sauran shafukkan idan har suka kiyaye da dokar kasar.

Ma'aikatar sadarwa da watsa labarai ta hanyoyin fasaha na zamani ta fada a wata sanarwa cewar "an bayyana cewa, kungiyoyi masu kiyayya ga kasa suna amfani da hanyar sadarwa ta zamani wajen jan hankalin matasa su shiga harkokin jihadi."

Ta cigaba da cewa babban abin damuwa ma shine masu shiga shafukkan dake aikewa da wasu bayanai ba su bukatar cika wata ka'ida don haka za su iya boye sunayen su.

Shafukkan guda hudu da aka sake budewa an ce sun tattauna da gwamnatin Idia ne a kokarin kawar da damuwar da ake da ita, duk da yake ba a tantance ba ko akwai wani canji da aka samu.

Wasu masu shiga shafukkan suna bayar da rahotannin cewar har yanzu sun gaza shiga shafukkan da aka ce an janye ma takunkumin.

Pranesh Prakash daga Cibiyar masu mu'ammala da Internet ta India ya ce, "duk wani wanda ke da tunani, zai ga cewa wadannan shafukka ba su tunzura ayyuka na ta'addanci.

Wasu mutanen dai sun yi tankiyar cewa, matakin da Indiar ta dauka sun saba ma fatar da kasar ke yi ta zama kasar da ta zarce kowacce kasa a duniya ta fuskar ayyukan fasaha.

Karin bayani