An ceci 'yan ci-rani a tekun Bahar rum

'Yan ci-rani da jirgin ruwan su Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan ci-rani da jirgin ruwan su

Daruruwan 'yan ciranin da suke makale a tekun Mediteranean a lokacin da masu fataucin mutane suka yi watsi da su, sun bar jirgin ruwan da suke ciki yanzu haka, bayan da aka janye shi zuwa kudancin italiya.

Kwamnadan masu gadin gabar- tekun a tashar jiragen ruwa ta CORIG-LIANO CALABRO, ya fadawa BBC cewa akwai 'yan gudun hijira 360 a cikin jirgin, kuma dukkaninsu sun fito ne daga Syria.

Ya ce an kwashe su a cikin motar safa zuwa sassan kasar Italiyan daban daban. sai dai yace dukkaninsu na cikin koshin lafiya.

Karin bayani