Al-Liby ya rasu kafin a fara masa sharia

Abu Anas al-Liby Hakkin mallakar hoto FBI
Image caption Abu Anas al-Liby

Al-Liby dai yana daya daga cikin wadanda ake zargi da kitsa harin bama bamai a ofisoshin jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania a shekarar 1998

Tun shekarar 2013 ne ake tsare da Al-Liby a Amurka, bayan da ya fada hannun dakarun kundubalar Amurka a Birnin Tripoli na Libya.

Amurkar ta sa sunan sa a cikin jerin sunayen wadanda take nema ruwa a jallo.

Harma ta ce zata bada tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya bada bayanan da zasu kaiga kama shi.

Sai dai mutumin ya ce bashi da hannu a tashin bama-baman da suka faru kusan a lokaci guda.

Lamarin dai ya hallaka sama da mutane dari biyu, kuma ya jikkata kusan mutane dubu biyar.