Ana ci gaba da binciken jirgin AirAsia

Iyalan wadanda suke cikin jirgin cikin jimami. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mako guda ke nan da faduwar jirgin a tekun Java na kasar Indonesia.

Kyawun yanayi da aka samu ya ba tawagar masu ninkaya a teku damar ci gaba da neman tarkacen jirgin AirAsia da ya fada cikin tekun Java a kasar Indonesia.

An gano wasu manyan abubuwa guda hudu a saman tekun, da ake kyautata zaton na daga cikin tarkacen jirgin.

Tun da fari rashin kyawun yanayi ya janyo tsaikon aikin binciken, sai dai ana sa ran samun yanayi mai kyawu cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Ana sa ran masu ninkaya a teku za su yi kokarin gano sassan jirgin da karin gawawwakin mutanen cikinsa, inda kawo yanzu aka fito da gawawwaki 30.

Hukumar hasashen yanayi a Indonesia ta ce mai yiwuwu rashin kyawun yanayi ne ya haddasa hadarin jirgin.