Mazauna Baga na tserewa Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP

Mazauna garin Baga da wasu kauyuka a arewacin Najeria sun tsallaka zuwa kasar Chadi mai makwabtaka, bayan wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai ranar Asabar.

'Yan bindigar, wandada ake zaton 'yan Boko Haram ne, sun farma garin cikin motoci da babura dauke da manyan makamai.

Mazauna garin sun ce sojojin da ke garin, da kuma 'yan banga sun ja daga da 'yan bindigar kafun daga bisani su fi karfin su.

Ba'a san wanda yake iko da garin kawo yanzu.

Yanzu haka dai, daruruwan 'yan garin ne da kuma wasu garuruwa suka tsere zuwa Chadi.

Daya daga cikin su ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa: " Sojoji da yawa sun yada makaman su sun gudu tareda da sauran jama'a."

Kawo yanzu dai rundunar sojin Najeriya bata ce komai ba akan harin.

Dan Majalisar Dattawan Najeria mai wakiltar arewacin Borno, Sanata Maina Ma'aji Lawan, inda yankin na Baga yake, ya shadawa BBC cewa jama'ar yankin na cikin mayuwajin hali.

A watan Afrilun 2012 ma an kai wani hari akan garin na Baga, lamarin da ya kaiga kone daruruwan gidaje a garin.

Kungiyar Boko na rike da garuruwa dadama a Jihar Borno.