Kenya: An tsinci gawar mai bada shaida

'Yan sandan kasar Kenya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan kasar Kenya

Mutumin dai shine babban shaida mai bada bahasi a shari'ar da ake yiwa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto a kotun duniya dake Hague.

Kafofin yada labarai na cikin gida a Kenya sun ce an tsinci gawar Menshach Yebei ne a kusa da wani kogi fiye da mako guda bayan da aka ga wasu mutane sun tasa keyarsa cikin wata mota mara lamba a garin Eldoret.

A kwanannan ne dai ake sa ran Mr Yebei zai tashi zuwa birnin Hague domin halartar cigaban shari'a akan mataimakin shugaban kasar William Ruto.

Mataimakin shugaban kasar na fuskantar tuhuma ne akan harin da aka afkawa 'yan kabilar Kikuyu dake yankin Kalenji a lokacin rikicin bayan zaben kasar Kenya shekaru bakwai da suka gabata.