Paparoma Francis ya nada sabbin Waliyyai

Sabbin waliyyai na darikar Katolika Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabbin waliyyai na darikar Katolika

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya cigaba da yunkurin garanbawul ga shugabancin chochin na Roman Katolika tare da nada sabbin waliyyai ashirin.

Paparoman yace an zabo waliyyan ne daga kasashe goma sha hudu wadanda suka hada da kasar Habasha da Thailand da kuma Tonga.

Sha biyar daga cikin sabbin waliyyan yan kasa da shekaru tamanin ne a duniya wanda ke nufin cewa za su iya shiga cikin majalisar da za ta zabi wanda zai gaje shi.