Gambia:An damke mutane kan yunkurin juyin-mulki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Yahya Jammeh ya shafe shekaru 20 a kan mulki

Gwamnatin Amurka ta tuhumi wasu mutane biyu da hannu a wani yunkurin juyin-mulkin da aka yi a kasar Gambia.

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta bayyana sunayen mutanen biyu watau Cherno Njie da Papa Faal.

Wakiliyar BBC ta ce "Takardun da aka gabatar wa kotu sun nuna cewa, a watan jiya ne mutum biyun suka yi bulaguro daga Amurka zuwa kasar Gambia da nufin tumbuke gwamnatin kasar, kuma da Cerno Njie za a nada shugaban kasa, da yunkurin juyin mulkin ya yi nasara."

Ana dai tuhumarsu a kotu da kitsa juyin mulkin da kuma mallakar makamai da nufin haddasa rikici.

Rahotanni dai na cewa gwamnatin kasar Gambia na ci gaba da tsare dangin wadanda ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulkin.