Lebanon ta fito da tsarin visa ga 'yan Syria

Wasu yara a sansanin 'yan gudun hijira na Lebanon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akalla mutane kusan mliyan daya ne suka tsrewa yakin da ake yi a Syria, tare da fakewa a kasar Lebanon.

Kasar Labanon za ta gindaya sabbin ka'idoji, da za su bukaci duk wani dan Syria samun Visa kafin ya shiga kasar ta.

Kawo yanzu akalla akwai kusan 'yan gudun hijira miliyan guda a cikin kasar ta Lebanon, wanda yawansu ya sanya kasar cikin wani hali na daban.

Wannan shi ne mataki na baya-bayan nan da gwamnatin Lebanon ta dauka, a kokarin ta na takaita yawan yan gudun hijirar Syria da ke kwarara cikin kasar, kawo yanzu 'yan gudun hijira na zaune cikin takura a sansaninsu, inda akalla mutane 50 ke kwana adaki guda saboda yawansu.

Haka kuma wata karin alama ce ta irin mawuyacin hali da 'yan gudun hijira zasu sake fadawa a kasar, wadda dama tuni take cikin takura mai tsanani.