An kai hari a sansanin soji a Mali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption wani jami'in tsaro na zargin cewa maharan na da alaka da kungiyar Alka'ida

Akalla mutune 5 ne suka rasa rayukansu a wani harin da aka kai kan sansanin sojin kasar Mali.

Da safiyar yau Litinin ne wasu 'yan bindiga cikin wata mota A-kori-kura, suka kai hari garin Nampala da ke kusa da iyakar kasar Mali da Mauritania.

Wani jami'in tsaro dai na zargin cewa maharan na da alaka da kungiyar Alka'ida.

A shekara ta 2012 ne wasu kungiyoyin 'yan tawaye suka mamaye yankin kasar Malin mai yawan gaske, amma daga bisani sojojin kasar Faransa suka fatattake su, amma duk da haka 'yan tawayen na ci gaba da kai hari daga lokaci zuwa lokaci.

Mali na cigaba da fuskantar barazana hare-hare daga kungiyoyin Alka'ida da Abzinawa.