Tattalin arzikin Nigeria zai shiga matsi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Matsalar faduwar farashin mai zata shafi kananan sana'o'i

A Najeriya, wasu masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa kasar ba za ta iya jure wa tasirin ci gaba da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ba.

Kimanin kashi 90 cikin dari na kudin shiga a Najeriya daga mai take samu.

Gwamnatin kasar ta yi kwaskwarima a kasafin kudin ta na bana da ta turawa majalisun dokoki har sau uku saboda matsalar faduwar farashin man.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka na jami'ar Bayero ya ce tun yanzu matsalar ta sa wasu gwamnatoci a kasar kasa biyan albashin ma'aikata.

Masanin ya ce akwai yiwuwar gwamnatin Najeriya ta sake fuskantar matsala a kasafin kudin nata wanda ta tsara a kan farashin gangar danyen mai dala 65, ganin yadda farashin ya kara faduwa zuwa dala 53.