'Jonathan bala'i ne ga Nigeria' - Limamin Coci

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da ake sukar lamirin gwamnatin shugaba Jonathan ba.

A Najeriya, wani babban limamin Roman Katolika a jihar Enugu, Reverend Father Ejike Mbaka ya caccaki shugaba Goodluck Jonathan da gazawa tare da cewa bai kamata ya sake tsayawa takara ba a zaben Fabrairu.

Wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa ta shafukan sada zumunta da muhawara, ya nuna babban limanin yana caccakar shugaba Jonathan da rashin iya gudanar da mulki.

Reverend Mbaka dai ya yi hudubar ta sa ce a gaban dubban 'yan cocin a jajiberen sabuwar shekara, yana mai cewa babu abin da ya kamata ga shugaba Jonathan illa ya sauka daga mulki saboda gazawarsa.

Yanzu haka dai fiye da mutane dubu 100 ne suka kalli bidiyon a shafin Youtube kadai, ban da wadanda suka kalla a whatsapp, da facebook da makamantansu.

Sai dai jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta bakin sakataren yada labaranta Barisster Abdullahi Jalo ta ce kalaman da limamin cocin ya yi bai da ce ba sam.

Ya ce Reverend Father Ejike Mbaka ya nuna wa duniya an saye shi da kudi ne domin ya zo ya kalubalanci jam'iyyar PDP da jagorancin shugaba Goodluck Jonathan.