An soma shari'ar maharin Boston

Dzokhar Tsarnaev, maharin Boston na Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dzokhar Tsarnaev, maharin Boston na Amurka

A Amurka, an gurfanar da Dzokhar Tsarnaev gaban kuliya, wato Ba'amurke dan asalin Checheniyar nan, wanda ake zargi da kai harin bom lokacin gasar tseren da aka yi a Boston.

Mutane uku ne dai suka mutu a shekara ta 2013 sakamakon harin.

Ana dai tuhumarsa da aikata laifuka talatin, amma bai amince da aikatawa ba.

Wanda ake tuhumar dai ka iya fuskantar hukuncin kisa: Wakiliyar BBC ta ce irin cincirindon da dubban masu taimaka wa alkali suka yi a wajen shara'ar, wata ishara ce cewa shara'ar na da nasaba da manyan laifuka.