Boko Haram: Ana zaman zullumi a Niger

Image caption Dubban 'yan Nigeria sun tsallaka Niger saboda 'yan Boko Haram

Jama'a a garuruwa a Jamhuriyar Niger na rayuwa cikin zullumi bisa fargaba kungiyar Boko Haram ka iya kaddamar da hari a kowanne lokaci.

Magajin garin Diffa, Hankaraou Biri Kassoum wanda ya bayyana hakan, ya ce a yanzu galibin garuruwan Nigeria da ke makwabtaka da Niger duk suna karkashin ikon Boko Haram.

Kassoum a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce wata rana 'yan Boko Haram za su iya kai musu hari.

Ya ce "Muna ganin yadda 'yan Boko Haram suka kafa tutocinsu a daya bangaren kan iyaka, kuma suna kara karfi a koda yaushe."

A yanzu haka akwai dubban 'yan gudun hijira daga Nigeria wadanda ke neman mafaka a Diffa.

A ranar Asabar ne 'yan Boko Haram din suka kwace sansanin dakarun kawance na kasashen Niger da Kamaru da Nigeria da ke gab da tafkin Chadi inda suka hallaka mutane da dama.