Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hadarin mota na yawan hallaka mutane a Masar

Masar na daya daga cikin kasashen duniya da ke kan gaba wajen yawan asarar rayuka a sakamakon hadarin mota.

Hukumar lafiya ta Duniya ta ce mutane dubu goma sha biyu ne ke mutuwa a kasar a kowacce shekara.

To wasu dai na dora alhakin al'ammarin a kan gangancin tuki, yayinda wasu kuma ke cewa rashin kyaun hanyoyin kasar ne.

Ga dai Aichatou Moussa da karin bayani: