Ana gangamin kin addinin musulunci a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gudanar da gangamin a birane 12 na kasar Jamus.

Dubban mutane a kasar Jamus sun bi ayarin masu tattaki da gangami na nuna goyon baya da na akasin haka ga wata kungiya dake adawa da abinda ta kira, yada musulunci a nahiyar turai.

Hukumomi a Cologne sun kashe wutar lantarki a wata babbar mujami'a a birnin, da kuma saman gadoji a Rhine, a zaman martani ga abinda magajin garin, Juergen Roters ya kira fargabar data haifar.

Ita ma Kathrin Oertel, ta kungiyar PEGIDA da ke jagorantar gangamin nuna adawa da yaduwar musulunci a kasashen yammaci, ta ce gwamnatin kasar ce ke da laifi, saboda rashin kyakyyawan tsarin shigar baki cikinta.

A gabashin birnin Dresden, mutane dubu 18 ne suka halarci gangamin kin jinin musuluncin, kuma shi ne gangamin mafi girma da aka yi zuwa yanzu.