"Matar Hamma ta yi wa 'yan sanda barazana"

Image caption Hama Amadou ya tsere daga Nijar

A Jamhuriyar Nijar, alkalin wata kotun Yamai ya zargi matar tsohon kakakin majalisar kasar malam Hama Aamadu, Hajiya Hadiza da yi wa 'yan sanda barazana.

Alkalin ya ce Hajiya Hadiza da tsohon gwamnan bankin SONIBANK Alhaji Musa Hayyatu sun yi wa 'yan sandan barazanar cin zarafinsu ne lokacin da suka hana su yin balaguro a ranar Asabar din da ta gabata.

Alkalin ya ce mutanen biyu za su gurfana gaban kotu a ranar 16 ga wannan watan domin su ba da bahasi dangane da zargin.

Ana tuhumar Hajiya Hadiza da mijinta da kuma wasu makusantansu da yin safarar kananan yara daga Najeriya, lamarin da ya sa Hamma Aamadu ya tsere daga kasar.