Gwamnati ta ki sakarwa INEC kudin zabe

Image caption INEC ba ta da isasshen kudin da za ta yi zaben 2015

Majalisar Wakilan Najeriya ta ce har yanzu bangaren zartarwa bai bai wa hukumar zaben kasar isassun kudin da za a gudanar da zaben 2015.

Shugaban Kwamitin Majalisar da ke kula da harkokin zabe, Jerry Manye ya shaida wa BBC cewa a an bai wa INEC naira biliyan 45 ne kawai a cikin na biliyan 120 da ta bukata domin gudanar da ayyukanta.

A cewarsa, yanzu akwai fiye da naira biliyan 75 da bangaren zartarwar ya kamata ya bai wa hukumar zaben idan dai ana so ta gudanar da zabe ba tare da matsala ba.

Hakan dai na faruwa makonni kalilan gabanin zabukan da za a yi a watan Fabrairu.

'Yan kasar dai sun zargi bangaren zartarwar da kin bai wa hukumar isassun kudi da zummar hana ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.