Intanet ta dauke a Perth saboda zafi

Hakkin mallakar hoto internet
Image caption Intanet ta dauke a birnin Perth har na tsawon sa'o'i 6 da rabi

Tsananin yanayin zafi ya tilasta wa daya daga cikin kamfanonin dake samar da hanyoyin intanet a birnin Perth na kasar Australia kashe na'urorinsa.

Kamfanin iiNet, wanda shi ne na biyu mafi girma masu samar da intanet a Australia ya ce ya kashe na'urorin ne a zaman matakin taka tsantsan, saboda zafin yanayin birnin ya kai maki 44.4 na ma'aunin Celcius.

Lamarin ya sa mutane da yawa sun rasa samun intanet na tsawon sa'o'i shida da rabi.

Daga baya mutane da dama sun bayyana rashin jin dadinsu ta shafukan sada zumuntansu na Twitter, inda suka nemi a fada musu dalilin haka.

Shugaban sashin fasaha na kamfanin iiNet Mark Dioguardi ya ce kamfanin ya fuskanci matsala da na'urorin sanyaya injinan samar da intanet din.

Ya ce ''wannan matsalace gami da yanayin zafi da ake yi suka sa muka kashe injinan".

Sai dai ya ce sun dauki mataki na tabbatar da cewa matsalar bata shafi kashi 98 cikin dari na masu mu'amala da su ba.

Matsalar daukewar hanyoyin intanet din ta shafi yammacin Australia, da sabon yankin arewacin Wales, da Victoria da kuma kudancin Australia.

Jama'a da dama sun yi kokarin lalubo wasu hanyoyin shiga shafukansu na Twitter da Facebook domin yin korafi a game da matsalar.