2015: An soki Jonathan kan nuna fifiko

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An hango Jonathan yana rawa a Kano a daidai lokacin da aka kai harin Nyanya.

Kungiyoyin fararen hula a Najeriya sun ce shugaba Jonathan yana nuna fifiko, don haka ne ma ya soke kaddamar da takarsa saboda mutuwar kanwarsa, amma bai yi hakan ba lokacin da 'yan Boko Haram suke kashe mutane a arewacin kasar.

A ranar Litinin ne dai jam'iyyar PDP ta ce ta soke kaddamar da yakin neman zaben shugaban da ta yi niyyar farawa a ranar a birnin Lagos saboda mutuwar kanwar shugaba Jonathan mai suna Nancy Jonathan-Olei.

Mai baiwa shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Farfesa Rufa'i Alkali shi ne ya shaida wa BBC matakinsu na dage gangambin zaben saboda Mr Jonathan na jimamin rasuwar kanwarsa.

Sai dai a martanin da shugaban kungiyar da ke sa idanu kan harkokin Majalisa, Malam Musa Rafsanjani ya shaidawa BBC cewa hakan ya nuna cewa "Shugaba Jonathan mutum ne mai matukar nuna son kai."

A cewarsa, "An kai hari a Nyanya da ke Abuja inda mutane da dama suka mutu.A lokacin ne aka sace 'yan matan Chibok, amma shugaba Jonathan ya tafi Kano yana rawa. Bai damu da mutanen da aka kashe ba."

Kazalika, Malam Rafsanjani ya ce an kashe mutane a Yobe, amma a dai dai lokacin ne shugaba Jonathan ya tafi bude bikin cikar shekaru 100 da hadewar arewaci da kudancin Najeriya.

Rafsanjani ya kara da cewa hakan, da ma wasu misalai da dama sun nuna cewa Mista Jonathan mutum ne da bai zai iya yi wa daukacin kasar adalci ba.