2015: MEND ta bukaci a zabi Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption MEND ta ce Jonathan ya daurewa masu cin hanci da rashawa gindi

Kungiyar masu fafutika ta yankin Naija Delta a Najeriya ta bukaci 'yan kasar su zabi dan takarar jam'iyyar adawa ta APC, Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015.

A wata sanarwa da kakakin kungiyar, Jomo Gbomo, ya fitar ya soki shugaba Goodluck Jonathan bisa rashin kawo ci gaba a kasar.

A baya dai shugaban ya kare kungiyar lokacin da ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai hari a Abuja yayin da ake bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yanci.

MEND ta kara da cewa shugaba Jonathan ya jefa kasar cikin mawuyacin halli, kuma ya daurewa cin hanci da rashawa gindi.

A cewar kungiyar, "Tun da Jonathan ya hau mulki, ya nada kwamitoci da dama domin yakar cin hanci, amma duk da rahotannin da suka gabatar masa bai dauki matakin dakile matsalar ba. Don haka ta ya ya za mu yarda cewa mutum kamar Goodluck Jonathan zai iya yakar cin hanci."

MEND ta ce Janar Buhari yana da cikakkiyar cancanta ta shugabancin Najeriya, don haka shi ya kamata a zaba.