Gwamnonin Jihohin dake fama da Boko Haram a Najeriya sun dage kan yin zabe

Gwamna Kashim Shettima na Borno
Image caption Gwamna Kashim Shettima na Borno

Gwamnonin jahohin Adamawa da Borno da Yobe a Najeriya sun bayyana cewar tilas ne a gudanar da zaben watan gobe a cikin jahohinsu.

Sun bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro tare da shugaban kasa Goodluck Jonathan kan tsaro a jihohinsu.

A bangare guda kuma babban hafsan hafsoshin tsaro na Najeriya Air Marshal Alex Badeh ya amsa cewar wani sansanin sojojin kasa da kasa ya fada a kan iyaka da Chadi ya fada hannun yan kungiyar Boko Haram.

Air Marshall Alex Badeh ya ce dakarun Najeriya ne kawai a sansanin a gabar tafkin Chadi a lokacin da yan Boko Haram din suka kwace shi ranar asabar.

Kasashen dake da suka yi iyaka da tafkin Chadin ne dai suka kafa rundunar kasa da kasar ce shekara dayar da ta wucedomin yakar ta'addanci da kuma fataucin makamai.

Da aka tambaye shi ko soja za su kwato sansanin, Air Marshall Badeh ya ce babu wani dalilin kin yin hakan.