Shugaban PDP ya ce ba adalci a jam'iyyarsu

Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Muazu ya ce ya kamata a sauya tsari a PDP idan aka lashe zaben 2015

Shugaban jami'iyyar PDP mai mulkin Najeriya, Ahmed Adamu Mu'azu ya ce babu adalci a cikin jam'iyyar.

Mu'azu, wanda ya bayyana hakan lokacin kaddamar da takarar shugaban kasar Goodluck Jonathan a Abuja, ya kara da cewa hakan ne ya sa 'yan jam'iyyar suka fice daga cikinta, kana suka koma jam'iyyar APC.

Ya ce, "babu adalci da raba daidai a PDP. Abin da ke faruwa a jam'iyyar shi ne 'Kura ke shan bugu, gardi na kwace kudi'. Ina so idan an ci zabe a daina hakan".

Mu'azu ya bukaci mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaba Jonathan da su jajirce wajen ganin jam'iyyar ta lashe zaben 2015.

A cikin 'yan shekarunan daruruwan 'ya'yan jam'iyyar PDP sun fice daga cikinta saboda abinda suka kira rashin adalci.

Daga cikin fitattun wadanda suka fice da PDP sun hada da Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwanso, Aminu Tambuwal, Rotimi Ameachi, Barnabas Gemade da kuma Aliyu Wammako.