An hallaka mutane 12 a ofishin mujalla a Paris

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda sun kaddamar da bincike kan lamarin

'Yan sanda a Faransa sun ce 'yan bindiga sun hallaka mutane akalla goma sha biyu a ofishin wata mujallar barkwanci mai suna Charlie Hebdo.

An kuma bayyana cewa wasu mutane biyar sun samu munanan raunuka a harin.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba inda 'yan bindigar da fuskokinsu a rufe suka kutsa cikin ginin sannan suka yi harbi kusan sau hamsin kafin su gudu a cikin mota.

'Yan sanda sun kaddamar da bincike domin gano wadanda suka yi aika-aikar.

A baya masu kishin Islama sun kai hari a ofishin mujallar da ke birnin Paris.

Shugaba Fran├žois Hollande ya ziyarci inda aka kai harin kafin ya kira taron gaggawa kan tsaro.