Faduwar darajar kaya a kasashen Euro

Hakkin mallakar hoto AFP

An dauki lokaci ana fargabar cewa kasashen da ke amfani da kudin Euron za su fuskanci wannan matsala ta faduwar darajar kaya, wadda kuma za ta yi illa ga tattalin arzikinsu.

Faduwar farashin danyen mai dai na daga cikin abubuwan da suka haddasa faduwar darajar kayan.

A ranar Laraba ne, farashin gangar mai ya fadi warwas zuwa kasa da dala hamsin, kuma rabo da a ga irin haka tun a shekara ta 2009.