An daure wata 'yar Ghana a London

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Safarar hodar Ibilis dai ta zama ruwan dare a duniya.

Wata kotu da ke birnin London ta yanke hukuncin daurin shekaru 8 a kan 'yar Ghanan nan, wacce aka kama ta da hodar ibilis.

Lauyoyin matar sun ce za su tilastawa kotun Ghana bayyana sunayen mutanen da matar ke taimakawa wajan safarar mugayen kwayoyin.

A ranara Talata ne dai a ka yanke wa matar mai suna Nayele Ametefe hukuncin, bayan kamata da kayi da hodar iblis mai kilo 12 wanda kudinta ya kai fiye fam miliyan 1.8 a London.

Ametefe dai ta ce manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnatin kasar Ghana ne ke sa ta yi musu wannan aiki tun shekarata 2004.

Ametefe na kan hanyarta ta zuwa jamhuriyar Dominican ne in da ta tsaya a London don yin sayayya da ganin likita.