Falasdinu za ta shiga kasashen kotun duniya

Ban ki-Moon Hakkin mallakar hoto
Image caption Samun damar zama cikin kasashen kotun ICC ga Falasdinu wata gagarumar nasara ce.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar cewa yankin Falasdinu zai zama cikin kasashen kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a ranar daya ga watan Afrilun wannan shekarar.

Sanarwar da ta fito daga Sakatare Janar na Majalisar, Ban Ki-Moon an wallafa ta ne a shafin intanet na majalisar a kan yarjejeniyar kasa da kasa.

Samun kasancewa cikin kasashen da ke cikin kotun duniyar wata dama ce ga Falasdinu ta gurfanar da Isra'ila a gaban kotun saboda aikata laifukan yaki.

Sai dai su ma mayakan sa-kai na Falasdinu ka iya fuskantar shari'a.

Shugaba Mahmood Abbas shi ne ya nemi kasarsa ta zama cikin kasashen kotun ICC a makon da ya gabata, wanda hakan ya tunzura Isra'ila har ta ki ba wa Falasdinu kudaden tafiyar da ayyukan gwamnati da suka tasamma dala miliyan 125.