Shell zai biya diyyar dala miliyan 84

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Matsalar malalar mai ta gurbata muhalli a yankin Naija Delta

A Najeriya, kamfanin mai na Shell ya amince ya biya diyyar dala miliyan tamanin da hudu ga al'ummar da malalar mai ta shafa a yankin Naija Delta da ke kudancin kasar.

An cimma wannan yarjejeniya ne bisa sulhuntawar da aka yi a wajen kotu, bayan da wasu lauyoyi a birnin London suka karbi shari'ar.

Masunta da manoma da matsalar malamar man ta shafa zasu samu dala dubu uku kowannensu a matsayin diyya, yayin da yawancin kudaden al'umar yankin Bodo ne za su ci gajiyar su.

Sulhun da aka cimma shi ne mafi girma irinsa a Najeriya, kuma ya kawo karshen shari'ar da aka shafe shekaru 3 ana yi.

Masu rajin kare al'ummomin Bodo sun ce kamata ya yi tun farko kamfanin na Shell ya amsa laifinsa.